Gwamnatin Gombe na shirin tsabtace sana’ar bola jari a bayan dawowar zaman lafiya jim kadan bayan hargitsi da zanga-zangar tsadar rayuwar ta haifar a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya ce gwamnatin za ta tsabtace sana’ar bola jarin ne don kauce wa ci gaba da aikata barna.
Njodi ya ce, majalisar tsaron jihar ta lura duk barnar da aka yi na kayayyakin al’umma, daga bisani an gano kayan ne a wajen masu harkar bola jari inda ake sayarwa don samun kudaden kashewa.
Ya ce a zaman majalisar an yanke shawarar zama da shugabannin kungiyar masu harkar bola jari domin bullo da hanyoyin da za’a magance ci gaba da barnata kayan jama’a da wasu Matasa batagari keyi saboda matsin rayuwa.
Zaman da akayi da Sarakuna da shugabanin kananan hukumomi da shugabanin hukumomin tsaro, ya gudana ne a gidan gwamnatin Jiha da nufin samar da sahihiyar hanyar samar da zaman lafiya.
A cewarsa, ba su so a yi zanga-zanga ba, amma da aka yi ta haifar da asara dukiyar gwamnati da ta al’umma.
Sannan Majalisar ta yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewar da suka yi wajen shawo kan masu zanga-zangar, hakazalika Gwamna Inuwa Yahaya bisa yadda ya tashi da kansa ya yi wa jama’ar gari jajen asarar da aka yi.