Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce sun shirya tsaf domin tabbatar da an gudanar da ingataccen zabe a shekarar 2023 mai zuwa.
Ya ba da tabbacin ne lokacin da yake jawabi a bikin yaye kuratan sojojin kasa da aka yi a makarantar kurata da ke Zariya, a jihar Kaduna ranar Asabar.
- Ya kamata Najeriya ta binciki zargin da ake yi wa sojojinta kan zubar da ciki – Guterres
- Mahara Sun Kashe Mutum 3 Sun Kona Gidaje 22 A Gombe
Aminiya ta rawaito cewa sabbin kurata 6,226 ne aka yaye daga makarantar horas da sojojin da ke Zariya.
Babban Hafsan ya bukaci sabbin kuratan da su kasance masu biyayya ga tsarin aiki da ladabi da kuma bin na gaba wurin tafiyar da muhimman manufofin rundunar sojin.
Faruk Yahaya, ya ce a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro, rundunar za ta ci gaba da iya bakin kokarinta don ganin sun kawar da sauran kalubalen da ke gabansu da kuma tabbatar da doka da oda a sassan iasar nan.
Daga nan sai ya yaba da kokarin da sarakuna iyayen jasa ke yi don cigaban ɓangaren tsaro da samar da zaman lafiy