Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince a kan shirya wata mukabalar ilimi tsakanin malamai da kuma Sheikh Malam Nasiru Kabara biyo bayan kalaman da malamin ya yi wanda ake zargi sun sabawa koyarwar addinin Islama.
Wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Jihar Kano Abba Anwar ya fitar, ta ce za a shirya zaman baje kolin dalilai na ilimi inda malamai daga bangarori da dama za su gabatar da hujjojinsu dangane da goyon bayan malamin a kan akidarsa ko sabanin haka.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwadago na Taraba
- An sako wakilin jaridar Punch da wasu mutum 2 da aka sace a Abuja
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 18 a Birnin Gwari
Sanarwar da hadimin gwamnan ya fitar ta ce nan da ’yan kwanaki kadan masu zuwa za a sanya rana da kuma wurin da za a gudanar da wannan tattaunawa wacce za a gayyato malamai domin su shaida daga ciki da wajen Jihar Kano.
Aminiya ta samu cewa sanarwar wannan mataki na zuwa ne bayan wata tattaunawa da Gwamna Ganduje ya yi tare da Kwamishinan Harkokin Ilimin Addini na Jihar Kano, Dokta Muhammad Tahar Adam da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Ali Haruna Makoda da kuma tsohon dan takarar Gwamnan Kano, Malam Salihu Sagir Takai da sauransu.
Kazalika, sanarwar ta ce Gwamnati Kano ta bayar da tabbacin samar da tsaro mai inganci a yayin mukabalar sannan ta amince a watsa ta kai tsaye a gidajen Rediyo na Jihar da na ketare.
Gwamnan yay i kita da al’ummar Jihar da su kwantar da hankulansu a yayin mukabalar ta kuma bayanta.
A makon jiya ne Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar Kabara, bisa zargin malamin da yin izgili ga Sahabban Manzon Allah (SAW).
Gwamnatin Jihar ta kuma rufe daukacin cibiyoyin karatu da majalisin Sheikh Abduljabbar, ta hana shi gabatar da wa’azi ko lakca; sannan ta dakatar da kafafen yada labarai daga sanya karatuttukansa ko hudubobi ko da’awa.