Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar sake rufe wuraren ibada muddin aka karya matakan kariyar cutar coronavirus a wuraren.
Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da haka a daidai lokacin da jihohi ke bude masallatai da coci-coci.
Bayan matakan tsafta da bayar da tazara, an kuma umurci masu rauni, ciki har da ‘yan shekaru 55 zuwa sama da kuma masu ciwon suga, zuciya ko kansa, da su ci gaba da yin ibada a gidajensu.
Mustapha, wanda kuma shine shugaban na kwamitin kar-ta-kwana da shugaba Buhari ya kafa domin yakar annobar coronavirus a Najeriya, ya ce kwamitin za ci gaba da wayar da kan jama’a game da ka’idojin bude wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.
Ya ce, “Mu na kara tunatar da jama’a game da matakan kariya da aka shardanta na bude wuraren ibada.
“An ba jihohi dokokin da Gwamnatin Tarayya ta tsara kuma muna sa ran shugabannin addini za su yi na’am da su.
“Dole ne a kiyaye su domin kauce wa yiwuwar jefa rayuwar jama’a cikin hadarin kamuwa da COVID-19.
“Muna kira da a yi taka-tsantsan a kowane lokaci.
- Abin da kungiyoyin addinai suka ce kan bude wuraren ibada
- An sassauta dokar hana ibada a masallatai da coci-coci
“Za mu rika sa ido kan yadda ake bin wadannan matakai da ma sake bullar cutar.
“Ba za mu yi wata-wata ba wurin janye sassaucin matukar akwai bukatar hakan don dakile yaduwar annobar.”
Wayar da kan al’umma
Mustapha ya kuma yi takaici yadda wasu ‘yan Najeriya da suka kamu da coronavirus ke kin killace kansu.
Don haka, ya ce wajibi ne a fadada wayar da kai zuwa kananan hukumomi musamman mafiya barazanar samun cutar.
Ta hakan ne a cewarsa za a iya daukar matakan gwaji da jinya a kan kari
Ya shawarci jihohi su dage wurin wayar da kan al’ummomi don ganin jama’a sun dabiantu da bin matakan kariya da kuma yin watsi da jita-jita ko tsangwamar wadanda suka kamu.
Jami’in ya jaddada muhimmancin yin amfani da shugabannin addini da sarakuna wurin wayar da kan jama’a game da annobar COVID 19.