Kamfanin sadarwa na MTN ya yi barazanar ficewa daga Nijeriya idan ba a bari ya ƙara kuɗin kiran waya ba don magance ƙarin kuɗaɗen gudanarwa da ke barazana ga ribar da yake samu.
Shugaban kamfanin, Karl Toriola ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara cibiyoyin MTN a Ibeju-Lekki a Jihar Legas.
- Ambaliya: Masarautar Kaltungo ta bai wa Borno tallafin kayayyaki
- Zargin Kwartanci: Babu hujjar an yi zina — Jami’in Hisbah
Ya ce ɓangaren sadarwa na asarar kuɗaɗe sosai kuma dole su ɗauki matakan gaggawa don magance hakan.
Toriola ya bayyana cewa MTN wadda ke da aƙalla mutum miliyan 78 da ke amfani fa layinsu, yana amfani da kuɗin da ya tara cikin shekara 20 da suka gabata.
Ya ce wannan yanayin ba zai ɗore ba.
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen gudanarwar kamfanin, musamman farahsin fetur da na dizal da ake amfani da su wajen samar da wutar cibiyoyin sadarwa, sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen da yake samu.
Shugaban ya jaddada muhimmancin inganta riba a ɓangaren sadarwa, inda ya yi gargaɗi cewa idan ba a ƙara kuɗin waya ba zai iya rufe ayyukansa.
“Ba wanda zai yi shakkar abin da na faɗa; idan ba a ƙara kuɗin kiran waya ba, za mu iya rufe kamfaninmu,” in ji shi.
Ya ce MTN na ɗaya daga cikin manyan masu biyan haraji a Nijeriya, amma a yanzu sun rage biyan haraji saboda matsalolin kuɗi da suka dabaibaye kamfanin.