✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin waya na shirin ƙara kuɗin kira da na data a 2025

Kamfanonin sadarwar na shirin ƙara kuɗin kiran waya da na data da na tura saƙonni a shekarar 2025

Akwai yiwuwar kamfanoni sadarwa za su ƙara kuɗin kira da na data da kuma tura rubutaccen saƙo a farkon shekarar 2025 mai kamawa.

Wani babban jami’in wani kamfanin da sadarwa ya bayyana cewa kamfanonin suna da ƙwarin gwiwar samun sahalewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) domin kara kuɗin kira da na data.

Jami’in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa kamfanonin sadarwar na MTN da Airtel da 9Mobile sun riga sun aika wa NCC da buƙatarsu kuma bisa dukkan alamu suna ganin haske.

Idan suna samu Hukumar NCC ta amince, buƙatar kamfanonin sadarwar na ƙarin kuɗin da suka shafe kusan shekara goma suna nema, ta biya ke nan.

Hukumar NCC ta ƙi amince wa kamfanonin ƙara kuɗi tun a zamanin tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami.

Kimanin shekara 10 ke nan yanzu kamfanonin suke neman ƙara kuɗi kira da na data da tura saƙonni, bisa dalilin hauhawar farashin kayayyaki, amma gwamnati tana ƙin ba su damar yin hakan.