✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu bar Nijeriya idan ba a bari mun ƙara kuɗin kiran waya ba —MTN

Shugaban ya ce kuɗin man fetur da na dizal sun ƙaru wanda hakan ke barazana ga ribar da suke samu.

Kamfanin sadarwa na MTN ya yi barazanar ficewa daga Nijeriya idan ba a bari ya ƙara kuɗin kiran waya ba don magance ƙarin kuɗaɗen gudanarwa da ke barazana ga ribar da yake samu.

Shugaban kamfanin, Karl Toriola ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara cibiyoyin MTN a Ibeju-Lekki a Jihar Legas.

Ya ce ɓangaren sadarwa na asarar kuɗaɗe sosai kuma dole su ɗauki matakan gaggawa don magance hakan.

Toriola ya bayyana cewa MTN wadda ke da aƙalla mutum miliyan 78 da ke amfani fa layinsu, yana amfani da kuɗin da ya tara cikin shekara 20 da suka gabata.

Ya ce wannan yanayin ba zai ɗore ba.

Ya ƙara da cewa kuɗaɗen gudanarwar kamfanin, musamman farahsin fetur da na dizal da ake amfani da su wajen samar da wutar cibiyoyin sadarwa, sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen da yake samu.

Shugaban ya jaddada muhimmancin inganta riba a ɓangaren sadarwa, inda ya yi gargaɗi cewa idan ba a ƙara kuɗin waya ba zai iya rufe ayyukansa.

“Ba wanda zai yi shakkar abin da na faɗa; idan ba a ƙara kuɗin kiran waya ba, za mu iya rufe kamfaninmu,” in ji shi.

Ya ce MTN na ɗaya daga cikin manyan masu biyan haraji a Nijeriya, amma a yanzu sun rage biyan haraji saboda matsalolin kuɗi da suka dabaibaye kamfanin.