Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a New York, inda ya bukaci kasashen biyu mafi girman tattalin arziki a Afirka su kara hada kai domin bunkasa tattalin arzikinsu.
Shugabannin na Afirka biyu sun hadu gabannin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda za a soma a wannan makon, a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
- Masarautar Katsina ta tuɓe rawanin Hakimin Kuraye kan ɗaurin auren mai HIV
- Za a soma Gasar Zakarun Turai lami babu Ronaldo da Messi
“Za mu iya hada kanmu ta yadda duka za mu amfanar da jama’ar mu,” kamar yadda Tinubu ya bayyana
Tinubu ya kara da cewa duka kasashen za su iya hada gwiwa ta fannin hakar ma’adinai da sadarwa domin “samar da ayyukan yi”.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta cire tallafin mai wanda ta ce kasar na matukar kashe kudi a kai da kuma cire takunkumin da gwamnatin baya ta saka kan hada-hadar kudaden waje.
Shugaban ya lashi takobin farfado da tattalin arzkin kasar wanda yake fama da bashi da hauhawar farashi.
A nassa bangaren, Shugaba Ramaphosa ya jinjina wa tsare-tsaren farfado da tattalin arziki wanda Shugaba Tinubu yake kan yi, inda ya yi alkawarin cewa Afirka ta Kudu za ta hada kai da Najeriya.
“Mu ne kasashe biyu mafi girman tattalin arziki a nahiyarmu kuma yana da kyau mu kara yaukaka dangantakar tattalin arzikinmu, musamman ta fannin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge,” in ji Ramaphosa.
“Muna so mu ga Najeriya da Afirka ta Kudu sun yi aiki kan abubuwa da dama saboda a duk lokacin da muka hada hannu, muna yin tasiri matuka a duniya ta hanyar matsayar da muke dauka ta hadin gwiwa,” a cewarsa.
Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu da ta bi sahun Najeriya wajen yin kira ga yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin taimaka wa Afirka wajen yakar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.