Rundunar Sojin Najeriya ta bayar da tabbacin kubutar da Leah Sharibu da sauran matan Chibok da ke hannun mayakan Boko Haram da ISWAP.
A karshen mako da ya gabata ne rundunar sojin ta jaddada kudirinta kan ceto Leah Sharibu, dalibar makarantar Dapchi da ta rage a hannun mayakan.
- Mun kashe ’yan bindiga 30 da suka kai wa sojoji hari a Abuja —DHQ
- LABARAN AMINIYA: ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikin Jami’o’in Najeriya Da Mako Hudu
Rundunar ta kuma sha alwashin ci gaba da kai hare-haren kan maboyar ’yan ta’addan da ke Arewa maso Gabashin kasar.
Manjo Janar Christopher Musa, Kwamandan rundunar Hadin Kai ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zayyana wa manema labarai wasu daga cikin nasarorin da rundunar ta samu kan ayyukanta na bayan nan a Arewa maso Gabas.
Janar Musu ya bayyana cewa, sun gurgunta kungiyoyin ’yan ta’adda ta yadda ba za su iya kai munanan hare-hare ba ko gudanar da ayyukan yaki da cin nasara ba.
“Muna kara zafafa bincike a kan kokarin ceto Leah Sharibu da sauran wadanda aka sace. Mun yi ta kubutar da mutanen da ba a ma samu labarin an yi garkuwa da su ba,” in ji Janar Musa.
Ya kara da cewa, “a yanzu sojojinmu suna shiga kowane yanki da ya zama mafaka ta sansanonin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
“Za mu ci gaba da matsawa har sai duk matan Chibok da sauran mutanen da aka sace sun kubuta daga hannunsu.”
Kwamandan ya kuma bayyana cewa, sojoji suna samun gagarumar nasara tun lokacin da aka fara aikin ba da agajin gaggawa na Operation Desert Sanity, tare da nuna cewa ba za a samu mafaka ga ’yan ta’addan da a halin yanzu sai mika wuya suke ga sojoji.
“Abin da muke yi shi ne hana Boko Haram da ISWAP damar samun muhimman kayayyakin ci gaba da gudanar da harkokinsu na rayuwa ba, muna kuma tabbatar da murkushe tattalin arzikin masu samar da kayan ayyukan ta’addanci.
“Misali ko a ranar 13 ga Yuli, 2022, lokacin da sojojinmu suka kama wani Haruna Fulani da Umaru da ake zargi da kai wa Ali Ngulde, Kwamandan ‘yan ta’addan kayayyaki a tsaunin Mandara da ke yankin Gwoza.
“Abubuwan da aka kwato a hannunsu sun hada da; yadi 30 na bakar auduga, rigar mata 25 da takalman roba da sauran kayayyaki,” in ji Janar Musa.
Sai dai Janar Musa ya yarda cewa ’yan ta’addan na ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a kan kananan al’ummomi masu zaman kansu da kuma wurare masu rauni ta fuskar tsaro.
Aminiya ta ruwaito cewa, Leah Sharibu daya ce daga cikin dalibai 109 da aka sace yayin da mayakan ISWAP suka kai hari Makarantar Gwamnati ta Mata da ke garin Dapchi a Jihar Yobe tun a ranar 19 ga Fabrairun 2018.
Sai dai yayin da an sako ragowar, mayakan sun ki sakinta kan abin da suka kira kin karbar addinin Islama a kokarin da suka yi na musuluntar da ita.