Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.
Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari a ƙaramar hukumar Tarmuwa a ranar 9 ga Afrilu, 2025.
- Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta
- Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi
A takardar sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya fitar ya ce, hedikwatar ’yan sanda reshen Dapchi da misalin ƙarfe 0500hrs, 9 ga Afrilu, 2025, ta cafke waɗanda ake zargin, ’yan ƙungiyar da suka ƙware wajen yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma neman barace-barace, suna gudanar da ayyukansu a ƙananan hukumomin Dapchi da Tarmuwa.
An dai alaƙanta waɗanda ake zargin da laifuka da dama da suka haɗa da: A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, masu garkuwar sun kai hari ƙauyen Badegana da kuma kai hari gidan wani da aka kashe, wanda ya yi sanadin rasa rai.
A ranar 10 ga Maris, 2025, waɗanda ake zargin sun karɓe N250,000 da ƙarfi daga Mudi Ibrahim na ƙauyen Askuwari, ƙaramar hukumar Tarmuwa, bayan sun yi barazanar sace shi ko kuma su kashe shi.
Waɗannan mutane sun amsa laifukan da suka aikata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a sashin bincike na jihar (SID).
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado ya ba da umarnin ci gaba da ƙoƙarin kama wasu ’yan ƙungiyar kuma ya buƙaci al’umma da su bayar da sahihan bayanai don taimakawa wajen gudanar da bincike.