✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kubutar da Kwamishinan da aka sace a Binuwai — ‘Yan sanda

An yi awon gaba da kwamishinan da hadimansa biyu.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Binuwai ta bayar da tabbacin cewa za ta ceto kwamishinan Muhalli da Raya Birane na jihar, Cif Dennis Ekpe Ogbu tare da wasu mutum biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa, a daren ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da Kwamishinan na Jihar Binuwai tare da hadiminsa da direbansa, a kan hanyar Ado zuwa Otukpo a jihar.

Rahotanni sun ce Ogbu na kan hanyarsa ta zuwa Karamar Hukumar Otukpo ne, inda wasu mahara suka tsayar da motarsa ​​kirar Hilux a mahadar Adankari a daren Lahadi, inda suka tafi da shi tare da mutanen biyu da ke motar.

Kakakin Rundunar a jihar, SP Catherine Anene, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ta ce jami’ansu na bincike kan lamarin.

Ta ce, “A ranar hudu ga watan Afrilun 2022 da misalin karfe 6:20 na safe a lokacin da jami’an ‘yan sanda ke sintiri, sai suka hangi wata mota da aka ajiye a wani dajin da ke kauyen Adankari, a hanyar Otukpo-Ado, daga bisani aka samu labarin cewa kwamishinan jihar Bunewai aka sace.

“Nan da nan aka tura tawagar ‘yan sanda domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai, CP Wale Abass wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya tabbatar da cewar za a ceto su”

“Yayin da yake tattaunawa da jama’ar garin Adankari, kwamishinan ‘yan sandan ya bukace su da su taimaka da sahihan bayanan da za su dakile miyagun laifuka a jihar.

“Kwamishinan ya kuma ziyarci ‘yan uwan ​​wanda abin ya shafa, inda ya ba su tabbacin cewa za a ceto mutanen da sauran wadanda aka yi garkuwa da su,” in ji Anene.