Dan Takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe kuma Sanatan Gombe ta Arewa, Alhaji Usman Bayero Nafada, ya ce bai ga fostarsa da ta ’yan PDP a yankin Gombe ta Kudu ba sai ta ’yan wasu jam’iyyu, don haka za su kwantar da duk fostar wani dan APC a jihar.
Sanata Bayero Nafada, ya ce al’ummar Tangale Waja da ke Gombe ta Kudu ba su da wata jam’iyya sai PDP, to me ya sa babu fostarsu sai ta ’yan APC a yankin?
Bayero Nafada ya bayyana haka ne a Kaltungo lokacin bikin raba wa mutanen yankin kayayyakin tallafi da ’yar majalisarsu, Hajiya Fatima Binta Bello ta yi, a kokarin da take yi na neman takarar Sanata daga yankin ana washegarin da za su karbi taron yakin neman zaben Shugaban Kasa na shiyyar Arewa maso Gabas na PDP a Gombe.
Nafada ya kara da cewa idan aka cire fostar ’yan APC mako mai zuwa, zai sake ziyartar yankin da kansa don ya tabbatar da cewa komai ya yi daidai wajen lika tasu fostar.
A jawabin, Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara kiran al’ummar Gombe ya yi cewa kada su zabi wanda ko kansila bai ta ba rikewa ba, dan takarar PDP ne ya fi cancantar zama Gwamnan Gombe.
Dagora, ya ce kada jama’ar Gombe su yi kuskuren da mutanen Bauchi suka yi na zaben da ya zama musu da-na-sani, domin yanzu a Bauchi ba abin da Gwamnan ya tsinana musu.
Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Mista Charles Iliya cewa ya yi Gombe ta PDP ce, duk wani abu na ci gaba da aka gani a jihar PDP ce ta kawo. Don haka bai kamata a yi wata jam’iyya da ba PDP ba.
Sannan ya ce APC ta gaza a matakin kasa, don ta kasa kawar da matsalar tsaro da rikicin makiyaya.
Daga nan sai ya ce Binta Bello ta fita zakka cikin ’yan siyasar Gombe domin ta yi abin da babu wanda ya taba yi a tarihin siyasar yankin baki daya.
Hajiya Fatima Binta Bello, ta ce ta raba kayayyakin tallafin ga al’ummarta ne don su shaida ribar dimokuradiyya, sannan kuma su zabe ta a zaben da ke tafe don ta zama Sanata.
Binta Bello, ta ce ta raba motoci 10 da Keke NAPEP 125 da babura 250 da kekunan dinki 150 da injunan markade 150 da kekunan aikin riga 50 da keken guragu 50 da injunan ban-ruwa150 da jannaretoci 40 da abin gyaran gashi na mata 40.