’Yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 22 na Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna, sun ce sun kashe biyar daga cikin daliban domin nuna wa gwamnati gazawarta kan cika sharudan da suka gindaya.
’Yan bindigar dai sun bukaci a biya su naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa, inda kwanaki uku bayan gaza cika umarnin nasu suka kashe uku daga cikin daliban da suka yi garkuwa da su da kuma karin wasu dalibai biyu daga baya.
- Mun kwato shanu 300 daga hannun barayi a dare daya – Gwamnan Zamfara
- Sun canza gida sau 18 a shekara uku saboda tsoron kyankyaso
’Yan bindigar sun ce za su ci gaba da yi wa daliban kisan dauki dai-dai lokaci bayan lokaci matsawar ba’a cika sharudan da suka bayar ba.
Sashen Hausa na muryar Amurka (VOA) ya ruwaito shugaban ’yan bindigar mai suna Sani Idris Jalingo yana cewa, muddin gwamnatin Jihar Kaduna da iyayen daliban da suka yi garkuwa da su suka gaza biyan kudin fansar tare da kawo musu babura masu kafa biyu kirar Honda guda 10 zuwa ranar Talata, za su kashe ragowar daliban da suke hannunsu.
Jalingo ya ce, Iyayen daliban tuni sun biya su naira miliyan 55 a matsayin kudin fansa.
“Mun ji kalaman gwamnan Jihar Kaduna cewa ba zai biya ’yan bindaga kudin fansa don kada su samu damar kara siyo wasu makaman.
“Ya fadawa Iyaye cewa shi ba zai biya kudin fansa ba idan aka yi garkuwa da mutum, don haka, muna so mu nuna gazawar gwamnatin Najeriya shi yasa muka kashe daliban,” a cewarsa.
Wasu dalibai biyu cikin wadanda aka yi garkuwa da su, wadan da suka yi magana sun bukaci gwamnati da Iyayensu da su dauki lamarin da muhimmanci.
Daya daga cikin daliban wanda daya ne daga cikin jikokin marigayi Sarkin Zazzau na 18, Shehu Idris, ya yi kira ga gwamnati da su daidaita da ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
“Tabbas za su aikata abun da suka fada saboda tuni sun kashe wasu daga cikinmu,” in ji dalibin mai suna Idris.
Ita ma wata daliba mai suna, Abigail Usman, ta bukaci gwamnati da ta turo kudin fansarsu don su samu su shaki iskar ’yanci.
Ta ce, “an kashe biyar daga cikinmu kuma a kan idonmu aka kashe su.
“Idan har basu samu kudin ba za su kashe mu gaba dayanmu,”in ji Abigail.
’Yan bindigar dai sun shiga makarantar ce a ranar 20, ga watan Afrilun 2021 bayan sun yi wa mai gadin Jami’ar kisan gilla.
Aminiya ta ruwaito Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da tattaunawa ko biyan ’yan bindigar kudaden fansar daliban.