✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu kashe N2bn kan tantance ma’aikatan makarantu —UBEC

Za a kashe kudaden wajen tantanc ma'aikatan makarantu a cikin kwana tara

Hukumar Kula da Makarantu a Matakin Farko (UBEC) ta ce za ta kashe Naira biliyan biyu wajen tantance malaman makarantu a cikin kwana 10.

Babban Sakataren Hukumar UBEC, Hamid Bobboyi, ya ce an ware kudaden ne domin tantance ma’aikatan makarantun a fadin Najeriya a shekarar 2022 da muke ciki

Ya ce hukumar za ta tantance makarantu a jihoi 17 na yankin Kudu da yankin Arewa mai jihohi 19 da kuma Birnin Tarayya, Abuja, daga ranar 4 zuwa 23 ga watan Yuli mai mkamawa.

Bobboyi ya shaida wa taron tantance ma’aikata da ya gudana a Abuja, inda ya ce rashin cikakkun bayanana ma’aikatan makarantu babban kalubale ne ga wajen aiwatar da shirye-shiryen ilimi.

Don haka ya ce tantance ma’aikatan ilimi da za a yi a bana zai ba da dama wajen samun cikakkun alkaluma da sauran bayanansu.

Ya bayyana cewa jami’an hukumar za su zaga makarantun firamare da kananan sakandare da ke matakin ilimi na bai-daya domin gudanar a aikin a fadin Najeirya.

A nasa jawabin, shugaban hukumar tantance ma’aikata ta kasa, Farfesa Bala Zakari, ya ce hukumar ta tattaro adireshin daukacin makarantun matakin farko a kowace karamar hukumar da ke Najeriya.

Ya kara da cewa an yi hakan ne domin tabbatar da kai wa ga makarantun da ke wurare masu nisa da masu wuyan zuwa saboda matsalar tsaro da sauransu.