Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce duk da nasarar da ta samu a Kananan Hukumomi uku a zaben da aka yi a Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Asabar, za ta bi kadin ragowar kujeru ukun a gaban kotu.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Iyorchia Ayu, ne ya bayyana hakan a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa ranar Litinin.
- Senegal za ta sanya wa filin wasa sunan Sadio Mane
- Ban ji dadin sanya hotona a labarin rikicin Kannywood ba – Rahama Sadau
Yana kalaman ne yayin bikin kaddamar da ginin kafafen yada labarai na Earnest Ikoli, a cikin shirye-shiryen wa’adi na biyu na Gwamnan, Jihar, Douye Diri.
Sai dai ya bayyana jin dadinsa kan yadda PDP ta lashe zaben a Kananan Hukumomin Birnin Abuja da Kewaye da Kuje da kuma Kwali.
Amma ya ce a shirye suke su kalubalanci sakamakon Gwagwalada da na Abaji da kuma na Kwali, wadanda APC ta yi nasara a cikinsu.
Shugaban jam’iyyar ya kuma yaba wa abin da ya kira namijin kokarin da Gwamnonin PDP suke yi a jihohinsu, wanda ya ce yana ba su kwarin gwiwar sake dawowar jam’iyyar mulkin Najeriya a 2023.