✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu inganta Musabaka a Jihar Bauchi – Baba Ilelah

Sabon Shugaban Kwamitin Musabakar Alku’rani na Jihar Bauchi Malam Mustafa Baba Ilelah ya yi alkawarin inganta gasar a jihar ta yadda masu gasar za su…

Sabon Shugaban Kwamitin Musabakar Alku’rani na Jihar Bauchi Malam Mustafa Baba Ilelah ya yi alkawarin inganta gasar a jihar ta yadda masu gasar za su rika yin koyi da aikata abubuwan da Alkur’ani yake umarni a yi.

Malam Mustafa Baba Ilelah ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce, “Bayan mun zauna mun yi nazari sai muka kudiri aniyar kauce wa kura-kuran da aka samu a baya, kuma muka yi niyyar inganta gasar karatun Alkur’anin ta yadda mahalarta gasar za su rika kokarin dabbaka abubuwan da Alkur’ani yake koyarwa, ba mutum yana karanta Alkur’ani ba ya aiki da shi ba.Domin an ce sau da yawa za ka samu mutum yana karanta Alkur’ani amma ba ya aiki da shi, kuma Alkur’ani yana la’antarsa.”

Shugaban ya bukaci mahalarta gasar da daukacin al’ummar Musulmi  su guji aikata abubuwan da Allah Ya hana su kuma rika aikata ayyukan alheri suna yin umurni da su domin samun dacewa a ranar Kiyama.

Ya ce suna shirye-shirye domin ganin sun fara gudanar da gasar a dukkan kananan hukumomin Jihar Bauchi, kuma wadanda suka zama zakaru a gasar kananan hukumominsu ne za su wakilci kananan hukumomin a gasar jiha wanda za a yi bana a Karamar Hukumar Ningi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Kwamishinan Kula da Harkokin Addinai na Jihar Bauchi Alhaji Ahmad Aliyu Jalam ya nanata kudirin gwamnati na goyon bayan harkokin addini a jihar.

Sai ya nanata muhimmancin Alkur’ani a matsayin littafin shiriya da yake shiryar da al’umma ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin ga kananan hukumomi 20 da ke jihar domin samun nasarar gasar a jiha baki daya.

Kwamishinan ya ce gwamnati mai ci ta kara fadin ma’aikatarsa ce da nufin inganta ayyuka, inda aka kara musu da sashen jin dadi da walwalar jama’a da hukumar kula da marayu da marasa galihu da hukumar shari’a ta jiha da kuma hukumomin ayyukan Hajji na Musulmi da Kirista.