Hukumar Hisbah ta sha alwashin daukar matakin ba sani ba sabo a kan duk mutumin da aka kama yana tozarta matan da ke sanya tufafi nau’in Abaya a Jihar Kano .
Hukumar ta bakin Babban Kwamandanta, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina ta ce daukar matakin ya zama dole duba da yawan korafin da mata suka kawo mata a sakamakon sanya Abaya a ’yan kwanakin nan.
- Mata sun yi zanga-zangar neman a halasta karuwanci
- El-Rufai na cijewa za mu yi yajin aikin gama-gari —NLC
Babban Kwamandan ya bayyana cewar ya zama wajibi mutane su gane cewar Abaya kalma ce ta Musulunci, bai kyautu mutane na yin dan kira ko tozarta matar da ta yi kwalliya ko ta sanya tufafin ba.
Ustaz Harun Ibn Sina ya bayyana cewa Abaya tana daga cikin nau’in sutura da Musulunci ya yarda mata su yi amfani da ita.