Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta gudanar da zabukan fitar da ’yan takara a mukamai daban-daban a watan Mayun 2022.
Wannan dai n zuwa ne makonni bayan da jam’iyyar da gudanar da Babban Taronta na kasa inda ta zabi tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugabanta na kasa.
- Majalisa ta yi wa kudirin daure ’yan daudu karatun farko
- Za a yi wa Blaise Compaore daurin rai-da-rai saboda kashe Thomas Sankara
Jam’iyyar ta ce za ta fitar da dan takarar shugaban kasa ranar 30 ga watan Mayu.
Za a fara zabukan ne da na ’yan Majalisar Dokoki na jiha a ranar 17 ga Mayu, yayin da na ’yan Majalisar Wakilai zai biyo baya ranar 19, sai kuma na ’yan Majalisar Dattawa ya gudana a ranar 21 ga watan na Mayu.
Zaben fitar da ’yan takara a mukamin gwamna zai gudana ne ranar 24 ga watan na Mayu.