Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala dukkan shirye-shirye na gina sabbin Asibitoci 484 a kananan hukumomi 44 da ke jihar da manufar bunkasa harkokin kiwon lafiyar jihar tun daga tushe.
Kwamishinan Kananan Hukumomin jihar, Alhaji Murtala Sule-Garo, ne ya bayyana hakan a birnin Dabo yayin zanatawarsa da manema labarai a safiyar ranar Talata.
Garo ya ce, za a kaddamar da aikin a karkashin shirin nan na tsarin kula da lafiya wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bijiro da shi na yi wa Banagaren Kiwon Lafiyar Jihar Garambawul mai taken ‘Health System Transformation Programme’.
Kwamishinan ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta fara gina sabbin asibitocin da inganta gine-ginen wadanda ake da su musanman a yankunan karkara da ke fadin jihar.
Ya kara da cewa, Gwamnatin ta kuduri aniyar gina manyan asibitoci masu cin gadaje 400 a sabbin masarautun jihar da aka kirkira kwanan nan da suka hada da Bichi, Gaya, Karaye da Rano.