Bayan karewar wa’adin takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata tun a shekarar 2015, Gwamnatin Kasar Iran a ranar Litinin ta ce ta fi karkatuwa zuwa ga sayar da makamai a madadin ta fita yin cefanansu.
Ministan Tsaro na kasar, Amir Hatami ne ya sanar da hakan da cewa tuni dama Iran da wasu kasashen suka kulla yarjejeniyar musayar makamai wajen saye ko sayar wa a duk sa’ilin da bukatar hakan ta taso.
- An ba mace ta farko babban mukami a Majalisar Shura ta Saudiyya
- Rikicin Azerbaijan da Armenia na iya shafar yanki –Iran
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito, Minista Hatami ya ce kowace kasa a duniya tana da ’yancin kare martabarta kuma ba za a bar Iran a baya ba wajen yin iyaka bakin kokarinta don ganin ta tsare mutuncinta.
Ministan ya ce a yanzu kasar tana da ikon samar da yawancin makaman da za ta wadatar da kanta domin tsaro, saboda haka za ta mayar da hankali ne wajen sayar wa mabukata a fadin duniya
Ya ce tun bayan da aka kakabata takunkumi hana mallakar makamai ne kasar ta mayar da hankali wajen kera na ta na kanta musamman manyan bindigogi, jiragen yaki na karkashi da kan ruwa masu amfani da fasahar harba makami mai linzami.
Yayin da a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta zare wa Iran takunkumin hana sayen makamai, Shugaban Kasar Hassan Rouhani ya sanar cewa daga yanzu kasarsa na damar mallakar makamai ta kowa ce irin hanya da ta ke so ba tare da wasu ka’idodi ba na kasa da kasa.
Sai dai shugaban cikin wani rahoto da jaridar BBC ta ruwaito, ya yi karin haske da cewa hakan ba ya nufin kasar za ta shiga sayen makamai ba ji ba gani.