✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu farfado da yankin Arewa maso gabas ta hanyar wakoki – Abubakar Sani

Abubakar Sani fitaccen suna ne a masana’antar wakokin Hausa, domin ya dade a cikin wannan sana’a. Shi ne ya yi wa Aminiya waka a shekarar…

Abubakar Sani fitaccen suna ne a masana’antar wakokin Hausa, domin ya dade a cikin wannan sana’a. Shi ne ya yi wa Aminiya waka a shekarar 2006. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa suna shirye-shiryen farfado da yankin Arewa maso gabashin kasar nan ta hanyar wasanni, yadda za su rika zuwa garuruwan da ke yankin suna gudanar da wasanni don dawo da walwalar mutanen yankin:

n Mawaqi, Abubakar SaniKo mene ne tarihin rayuwarka a takaice?
An haife ni a garin Kano, a kramar Hukumar Gwale. Na yi karatuna na firamare da sakandare duk a Kano. Bayan na kammala ne sai na sami gurbin yin karatun diploma a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi. Bayan na gama sai na shiga harkar wasan kwaikwayo na Hausa.
Ya aka yi ka fara waka?
Zan iya cewa da rana tsaka na fara waka, ban taba yin waka ina karami ba. Kamar yadda na gaya miki, kafin na fara waka na fara shiga masana’antar fina-finan Hausa, inda na fito a yawancin fina-finan Kamfanin Iyantama Multimedia. Na fito a fina-finai irin su ‘Fallasa’ da ‘A’isha’ da ‘Mutu-Ka-Raba’ da sauransu. A lokacin da nake aiki a Kamfanin Iyantama sai aka ba ni manaja mai kula da situdiyon kamfanin. To zamana a wannan wuri ne ya sa na fara waka. A lokacin ma ban dauki abin a matsayin sana’a ba, kamar dai na dauke shi a matsayin sha’awa. A yau dai zan iya cewa na kai shekara 15 zuwa 16 ina yin waka amma da yake Allah Shi yake da komai a hannunSa sai ga shi ta kai na ajiye harkar fim gaba daya, inda kuma na shiga harkar waka gadan-gadan. Daga cikin wakokin da na yi a fim sun hada da na ‘Jadawali’ da ‘Tutar So’ da ‘Zakka’ da ‘Babban Gari’ da sauransu.
‘Shin masu fim ne ke kiranka ka yi musu waka ko kuma idan ka yi wakar kai kake kai musu su biya ka?”
Yawanci dai masu fim din ne ke sanyawa a yi musu waka, inda za su kawo labarinsu sai mu kalli lamarin sannan mu yi musu waka. A wasu lokutan kuma sai sun ji wakar sannan suke samunbasira a kan abin da za su yi fim a kai.
Baya ga wakokin Hausa kana yin wasu wakoki?
E, ina yin wakoki a kan abin da ya shafi bangaren siyasa da fadakarwa da wakokin aure da sauransu. A yanzu haka ma ina da albam har guda hudu da suka kunshi wakokina; akwai irin su ‘Ganga Sa Waka’ da ‘Sirrin Waka Da Wake’ da ‘danhausa.’ Haka kuma nakan yi wakokin tallace-tallacen kamfanoni daban-daban. Ba na mantawa ma, a shekarar 2006 na yi wa jaridar Aminiya waka.
Ana ganin kamar rashin hadin kai da ke tsakaninku mawaka shi ya sa kuka kasa kafa tsayayyar kungiya, me za ka ce a kan hakan?
Zan iya cewa wanann magana ba gaskiya ba ce, duk da cewa akwai kungiyoyi masu yawa na mawaka a Kano, amma kowa ya san babbar kungiyarmu ita ce ta Inuwar Fasaha, wacce yawancin mawakan da suka dauki waka a matsayin sana’a suke cikinta. Kin san akwai wasu mutanen da ke daukar abin da suke yi da wasa. To irin wadanan su ne ba su shiga kungiya. Su dai kawai sunansu neman, da zarar sun samu burinsu ya cika. Mu muna ganin sai mutum ya dauki sana’arsa da muhimmanci yake shiga kungiya. A kungiyarmu muna da hadin kai, idan wani abu ya taso mukan yi kokarin yin abubuwa tare ba tare da wariya ba.
Wacce shawara kake da ita ga ’yan uwanka mawaka?
Ina shawartarsu da su zama masu yin aiki da hankali, mu
ajiye duk wani abu na jahiliyya, irin su habaici da yi wa junanmu hassada. Duk duniya akan samu hassada a tsakani amma dai kamata ya yi mu ajiye komai a gefe, mu hada kanmu. Haka kuma akwai bukatar mu rika tsaftace kalamanmu a wakokinmu.
Wane buri kake da shi a harkar waka?
A yanzu dai zan iya cewa babu abin da na sa a gaba, na ga ya tabbata a wannan harka, illa wani kuduri da nake da shi wanda nake fatan tabbbatuwarsa. Kodayake wannan ba wai tunanina ni kadai ba ne. Muna shirye-shiryen ganin cewa mun farfado da yankin Arewa maso gabashin kasar nan tare da dawo da walwala da nishadi ga mutanen.
Yankin, duba da irin yanayin tashin hankali da suka shiga a baya. Kowa ya san yadda rigingimun ’yan tada kayar baya ya ruda bangaren Arewa maso gabashin kasar nan, musamamn ma Jihar Borno. Wannan abin ya sa har yanzu mutane sun ki sakin jikinsu da yankin ta harkokin kasuwanci da sauransu. Har yanzu mutane ba su son abin da zai kai su wanann yanki, duk da cewa an sami zaman lafiya da tsaro a yanzu. Duk wanda ya je wanan yanki zai dawo yana gaya maka kyakkyawan labari game da ci gaban da aka samu a yanzu amma duk da hakan mutanen sun ki sakin jiki su koma da harkokinsu a wannan yanki. Muna so mu rika zuwa wannan yanki muna gudanar da harkar wasa, ba wai kawai na waka ba har su wasannin kwallon kafa da sauransu. Zuwan da za mu yi mu yi wasanni a wurin shi zai kara tabbatar wa jama’a cewa an samu zaman lafiya a yankin. Sannan a gefe guda mu dawo da walwalar da mutanen yankin suka rasa sakamakon halin da suka shiga a baya. Wasu sun rasa iyayensu da iyalasnu; wasu kuma sun rasa dukiyoyinsu. To muna so mu kawar musu da damuwarsu. A yanzu haka abin da muke kokarin yi shi ne mu nemi yardarm Ma’aikatar Harkokin Matasa Da Wasanni ta kasa, idan har wannan kuduri namu ya sami karbuwa a wajen gwamnati da kuma jami’an tsaro, za mu yi kokari mu ba wa kasarmu gudummawa ta hanyar sana’armu, yadda za a sake farfado da yankin Arewa maso gabashin kasar nan. Idan har gwamnati ta yarda za ta fito mana da hanyoyin da za mu gudanar da wanann kuduri namu cikin nasara. A tunainmu dai abin zai taimaka ya tabbatar wa jama’a cewa zaman lafiya ya samu a yankin.
Zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga ’yan uwana mawaka da su zo mu yi wanann tafiya tare. Sannan kuma akwai wani kuduri da muke da shi, inda mawaka za mu hadu mu yi wasu wakoki na yin kira ga kungiyoyin duniya da su zo su tallafa wa ’yan gudun hijira a kasar nan, wadanda yakin ’yan tayar da kayar baya ya raba su da matsugunnansu. Muna da yakinin cewa idan har muka yi wadannan wakoki, za mu sami biyan bukata, in sha Allah.
Waka tana da tasiri a rayuwar al’umma, mawaki yakan iya tabbatar da zaman lafiya ko tayar da fitina a cikin al’umma. Allah Ya ba shi wannan damar a hannunsa. Ba na mantawa akwai wani mawaki, Muhammad Nadir a kasar Sudan, ya yi amfani da waka wajen dawo da zaman lafiya a yankin, a lokacin da kasar Sudan ta shiga rudani.  A cikin wakokinsa ya nuna wa jama’a darajar kasarsu da jinsinsu da ’yan uwansu. Wannan waka da ya yi ita ta sa ’yan tawayen kasar suka ajiye makamansu, suka daina fada.