✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu dauki mataki kan manyan da suka saye filaye a Mambila ba su raya ba – Dokta Jedua

Yankin Mabila mai tsaunuka da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba wuri ne mai ban sha’awa da ya dace da noma da kiwo da…

Dokta Jedua DavidYankin Mabila mai tsaunuka da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba wuri ne mai ban sha’awa da ya dace da noma da kiwo da yawon shakatawa, amma an bar shi a baya. Wakilinmu ya ziyarci yankin inda ya gana da shugaban karamar hukumar Dokta Jedua Dabid a Gembu dangane da abubuwan da yankin ke bukata don ciyar da shi gaba:

Aminiya: Wane mataki kuke dauka don bunkasa yankin Mabila na jan hankalin jama’a su zo su ga irin albarkar da Allah Ya hore wa yankin?
Dokta Jedua: Kowane lokaci muna jan hankalin mutane su kawo ziyara a duk inda muka hadu da su don su ga yanayin wurin ko da za su bukaci zuba jari a fannin noma ko kiwo ko kamfanoni da sauransu. Idan mutane suka zo daga wasu jihohi sukan yi mamakin albarkatun da yankin Mabila ke da su kuma ana ba su shawarar su himmatu wajen bunkasa yankin don samar da ingantattun wuraren yawon shakatawa kamar yadda suke a duniya. Mutane suna zuwa daga jihohin kasar nan musamman Legas da Abuja da kasashen ketare don gane wa idonsu albarkar da Allah Ya yi wa wannan wuri kamar yadda suke ji. Koyaushe muna tattaunawa da gwamnatin jiha da ta tarayya don habaka wannan wuri ta yadda mutane za su zo su sa hannun jari a fagen yawon shakatawa.  Ko a kwanakin baya Gwamna mai riko Alhaji Garba Umar ya turo wasu baki masu sa jari a wannan harka, haka Gwamna danbaba Suntai lokacin yana da lafiya duk mako daya ko biyu sai ya ziyarci wannan yanki don bunkasa shi. Ba mu da matsalar tsaro a yankin muna zaune lafiya illa dan abin da ba a rasa ba na ayyukan ’yan fashi da makami da ake kokarin shawo kan lamarin. Amma babu rikicin kabilanci ko na addini tunda aka zabi Sarkin Mabila sai komai ya daidaita kai ya sake haduwa zaman lafiya ya inganta. Kuma wannan yanki yawanci za ka ga gida ana hade da Musulmi da Kirista da wanda bai ma damu da addini ba. Akwai kokarin kafa madatsar ruwa ta Mabila da ake yi wanda idan aka kammala za mu iya bayar da wuar lantarki ga wasu jihohi da kasashen makwabta.
Aminiya: Yaya za ka iya bayyana halin da yankin Mambila mai dogon tarihi ke ciki a yanzu?
Dokta Jedua: Yankin Mabila mai saunuka wuri ne da muke gode wa Allah da Ya ajiye mu a cikinsa, muna yi maSa godiya saboda ba abin da ba mu da shi a wannan tsauni, duk Najeriya ba wuri mai tsaunuka kamar Mabila, muna da abubuwa kamar sanyi mai ni’ima babu zafi babu sauro muna da yanayi mai kyau. Kuma idan ka hawo daga Serti zuwa Maisamari za ka ga
wurin yana ba ka sha’awa kamar kana kasar waje. Muna da kwazazzabai masu ban sha’awa da albarkatun kasa amma duk ba a tono su ba. Kuma wuri ne da idan aka zuba jari dole ya rayu a samu amfani mai yawa, domin ya kai kowa ya zo yawon shakatawa daga kowace kasa ta duniya. Saboda ya fi dajin Obudu nesa ba kusa ba saboda Obudu wani dan yanki ne na tsaunin Mabila.
Aminiya: Ina gaskiyar cewa manyan mutane sun saye filaye a nan ba su inganta su ba mutanen kasa kuma ba su amfana ba?
Dokta Jedua: Wannan magana gaskiya ce akasarin tsofaffin shugabannin kasar nan duk suna da filaye a nan har wadanda suka rike manyan mukamai, amma yawanci sun saye wuraren mutanenmu sun rasa wurin noma sai daga baya-baya muke ganin wasu kadan suna zuwa suna raya wurin ta hanyar ginawa da kuma killace wurin kiwon shanu. Amma akwai wadanda sun saye filayen yankin sun ajiye ba abin da suke yi ba su bude kamfani ko otel ko gina gidaje ko gidan gona ba, babu wani amfani da suke yi mana. Yanzu haka muna shirin tuntubar wasu manyan mutane da suka saye manyan filaye suka killace ba tare da raya wurin ba muna son jan hankalinsu su zo su raya ta hanyar noma ko kiwo ko gina makaranta don mu ci gaba. Idan ba haka ba kuma sai mu san matakin da za mu dauka koda kuwa na shari’a ne, ba za mu bari matasa su tashi kara-zube ga filaye masu albarka ba su da ikon cin gajiyarsu ba har ya zamo ana sa-in-sa da su kamar yadda ke faruwa a wasu sassa ba. Ko a kwanaki gwamnatin jiha ta kawo mana manyan makarantu nan haka Gwamnatin Tarayya ta kawo mana makarantar gona da wasu ayyukan ci gaba, amma saboda mutanen sun rike filayen ba su raya ba sai mun sha wahala sosai kafin muke samun wurin da gwamnati za ta yi ayyukan ci gaba saboda manya sun handame filayen sun hana tabawa.
Aminiya: Kasancewarka likita yaya za ka bayyana halin da ake ciki game da kiwon lafiya?
Dokta Jedua: Ni likita ne na fida saboda ina aikin likita a wani wuri na dawo nan ina aikin likita don taimakon mutane ina yi musu fida kyauta ina duba su kyauta, shi ya sa suka ga ya dace su zabe ni Shugaban karamar Hukumar Sardauna. Ba mu da cututtuka masu yaduwa a nan saboda muna da ruwan sha mai tsabta, ba mu da zazzabin maleriya ba mu da sauro ba mu da Poliyo. Muna son a kawo mana wata babbar makarantar kiwon lafiya saboda akwai nisa a fita don yin karatu ya wuce kilomita 600 zuwa Jalingo daga nan. Don haka idan yaranmu suka gama sakandare suna zama ne kurum ba abin yi.
Aminiya: Me kake ganin gwamnati za ta yi don bunkasa wannan yanki?
Dokta Jedua: Muna kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya su kawo mana dauki, su ma masu hannu da shuni su zo su sa jari a bunkasa arzikin karkashin kasa da yawon shakatawa. Idan akwai kudi muna son a gina otel-otel a gyara hanyoyin shiga dajin don yawon bude ido, a gina mana filin jirgi da hanyar da ta iso nan daga Bali don ba ta da kyau, muna da wuraren tarihi da yanayi mai ban sha’awa don haka ya kamata su rika zuwa suna gane wa idonsu.