Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) shiyyar Owerri ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin da ta shafe tsawon lokaci tana yi har sai bukatunsu sun biya.
Ta bayyana yajin aikin a matsayin na karshe da za ta sake yi a nan gaba.
- Yajin aikin ASUU ya sa matasa zaman kashe wando —Sarkin Musulmi
- Har yanzu ba mu cimma matsaya da gwamnati ba —ASUU
Shugaban kungiyar shiyyar Owerri, Uzo Onyibinama ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da ‘yan jarida a Jami’ar Nnamdi Azikiwe dake birnin Awka na jihar Anambra a ranar Talata.
Uzo ya ce, “Mun gaji da yajin aiki, wannan shine yajin aikinmu na karshe, shi yasa ba za mu janye shi ba har sai bukatunmu sun biya.
“Ba ma son a ce bayan wannan nan gaba kuma mu sake tsunduma wani yajin aikin, mun gaji da wannan wasan buyan. Wannan shine na farko kuma na karshe.
“Gwamnatin Tarayya ta dade tana dura wa mutane karairayi tare da kin cika alkawuran da ta dauka, ba wai maganar tsarin biyan albashin IPPIS ba.
“Har yanzu alal misali gwamnatin ta ki yarda ta aiwatra da yarjejeniyar fahimtar juna ta 2009 ba.
“Batun IPPIS wani sabon salo ne da aka fito da shi domin a kawar da hankalin mutane daga ainihin abubuwan da suke faruwa. Babu wata jami’a a duniya da take tafiya kan irin wannan tsarin.
“A iya sani na, babu wata matsaya da muka cimma da gwamnati. Kamata yayi su fito su ba mutane hakuri ba wai wasa da hankalin ‘yan kasa ba,” inji shi.
ASUU dai ta shafe kimanin watanni tara tana yajin aiki saboda rashin cimma wata kwakkwarar matsaya tsakaninta da Gwamnatin Tarayya.