Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna kuma Daraktan Cibiyar Arrayan Sheikh Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman, ya bayyana cewa Cibiyar Arrayan na shirye-shiryen bude Jami’ar Karatun Alkura’ani Mai Girma ta hanyar intanet, don saukaka wa al’ummar Musulmi koyon karatun Alkura’ani.
Sheikh Muhammad Sulaiman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a garin Jos.
“Mun yi tunanin mu bude wannan jami’a ta koyon Alkura’ani Mai Girma ta yanar gizo ce ganin cewa al’umma da dama za su amfana,” inji shi.
Ya ce ganin cewa intanet a Najeriya ba ta da karfi sosai, “don haka muka hadu da wasu jami’o’i da ke kasashen Turkiya da Azarbaijan da za su taimaka mana ta hanyar yanar gizo.”
Sheikh Muhammad Sulaiman ya bayyana cewa a wannan tsari, za su yi manhaja da za ta hada dalibi da malamin da zai karantar da shi.
Kuma dalibin zai ga malamin, shi ma malamin zai ga dalibin kuma duk karatun da dalibin yake yi, malamin zai rika yi masa gyara. Sannnan kowane karatu awa daya ne za a rika yi a kullum.
“Duk wanda yake son ya shiga, zai yi amfani da wayar hannunsa ce, idan lokacin shiga aji ya yi, sai ya kebe waje ya shiga ajin, ya yi karatunsa malami ya yi masa gyara.
“Za mu bude cibiyoyinmu a Kaduna da Jos da Kano da Gombe da Bauchi da dukkan inda ake da bukata a Najeriya.
“Wadanda ba su da manyan wayoyi, za su iya zuwa cibiyoyin da za mu bude su yi rijista, su rika zuwa suna yin karatu.”
Ya ce yadda mutum ya diba, haka za a yi wajen gudanar da wannan karatu.
Don haka da ma’aikata da ’yan kasuwa da mata a gida, ko mutum bai taba yin karatun Alkur’ani ba, zai iya shiga wannan jami’a.
Ya ce zuwa yanzu sun fara horar da jami’an da za su lura da wannan jami’a.
Sannan kuma sun samu malamai daga kasashen Saudiya da Amurka da Ingila.