Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya musuluntar da mutum 150 a garin Takai da ke Jihar Kano.
Da yake ba su kalmar Shahada, Sarkin, ya bayyana musu cewa daga lokacin da suka karɓi Addinin Musulunci, sun zama cikakkakun Musulmai.
- Malamai sun shiga yajin aiki kan rashin biyan su sabon albashi a Abuja
- ’Yan bindiga sun rage kudin fansar kananan yaran da suka sace a Kaduna
Ya ce, “Ku ci gaba da wannan aiki mai kyau, Allah zai saka muku da lada mai yawa.”
Wannan lamari ya faru ne a wajen buɗe sabon Masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje, ta gina a garin.
Ya kuma gargaɗe su kan yin sallah, bayar da zakkah, yin Azumin watan Ramadan, sannan su yi aikin Hajji idan Allah Ya ba su iko.
Sarkin, ya kuma roƙi gidauniyar Ganduje, da ta samar da malamai da za su koyar da su yadda za su yi ibada.
A jawabin Sarkin, ya yaba wa ƙoƙarin kwamitin Da’awa na gidauniyar Ganduje, kan ayyukansu na yaɗa Addinin Musulunci a lungu da saƙo na Jihar Kano da wasu jihohi.
Babban Sakataren yaɗa labarai na sarkin, Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, ya ce wannan abu ya ƙara ɗaukaka darajar Addinin Musulunci a Kano, tare da nuna cewa gidauniyar Ganduje na taka rawar gani wajen ɗaukaka Musulunci.