Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Ramadan, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin mai cike da falala, tausayi, da zaman lafiya.
A sakon da MDD ta fitar ta hannunsa, Guterres ya ce, “Ramadan lokaci ne da ke karantar da kyawawan ɗabi’u na tausayawa, taimakekeniya, karamci, da mutunta juna. Wannan wata dama ce ta ƙara hada kai, sada zumunta, da gina al’umma mai cike da zaman lafiya.”
Ya kuma jaddada muhimmancin tunawa da waɗanda suke cikin hali na ƙunci, musamman ’yan gudun hijira da waɗanda ke fama da rikice-rikice a wurare kamar Gaza, Sudan, da yankunan Sahel.
Guterres ya bayyana damuwarsa kan halin da suke ciki, yana mai cewa, “Ina tare da ku a wannan lokaci mai albarka, kuma ina roƙon samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gare ku.”
- Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna
- Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda
- NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan
Ya yi kira ga al’umma da su yi amfani da wannan wata mai alfarma wajen haɗa kai da tabbatar da zaman lafiya.
“Zaman lafiya shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma ya kamata mu yi aiki tare don gina duniya mai cike da adalci da mutunta juna,” in ji shi.
Sakatare Janar ɗin ya kuma bayyana cewa a kowanne Ramadan, yana yin azumi tare da al’ummar Musulmi a faɗin duniya, abin da ke ƙara masa fahimtar kyawawan dabi’u na Musulunci da kuma ƙwarin gwiwa.
A karshe, Guterres ya yi fatan Allah Ya karɓi ibadar al’ummar Musulmi yayin da suke azumtar wannan wata mai albarka, yana mai cewa, “Ina taya ku murnar wannan lokaci mai cike da albarka da tausayi.”