Gwamnatin Tarayya za ta riƙa biyan kamfanin Julius Berger Naira biliyan 280 domin kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa a duk wata za a biya kamfanin Naira biliyan 20 har na tsawon watanni 14 domin kamfanin ya kammala aikin kilomita 82 na ɓangaren ya rage a titin.
Ministan ya sanar da biyan wannan Naira biliyan 280 ne a yayin da yake kokawa kan ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukan hanyoyin.
Ya bayyana haka ne a wani zama da ya yi da Julius Berger kan ayyukan kwangilan manyan tituna da kamfanin yake gudanarwa, waɗanda Gwamnatin Tinubu ta gada.