✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ba masu yi mana kallon hadarin kaji kunya a bangaren tsaro – Matawalle

Ya ce masu fadar haka ba su san ma mene ne tsaro ba

Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya sha alwashin za su ba masu cewa ba su san tsaro ba kunya.

Mutane da dama dai sun yi ta sukar lamirin mukamin da aka ba tsohon Gwamnan na Zamfara, saboda yadda jiharsa ta sha fama da matsalar tsaro lokacin da yake jagorantar ta.

Sai dai Matawalle ya ce yana da kwarin gwiwar za su yi aiki tukuru wajen samar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.

Da yake jawabi a yayin wata liyafar da aka shirya masa domin taya shi murna a Abuja, ya ce, “Na ji wasu mutane na ta korafin cewa dan uwana Badaru Abubakar (Ministan Tsaro) da ni ba mu da kwarewar da za mu tafiyar da harkar tsaro a Najeriya. Irin wadannan mutanen ba ma su san mene ne tsaro ba.

“Saboda haka ba a nan gizo yake sakar ba, abu mafi muhimmanci shi ne jajircewa da mayar da hankali da kuma sadaukarwa.

“Lokacin da nake Gwamnan Zamfara, mun dauki dukkan matakan da suka kamata domin samar da tsaro a cikinta. Akwai lokacin da muka taba shafe tsawon kwana 100 ba tare da wata matsalar tsaro ba.

“Dukkan matakan da muka dauka sun yi tarihi sosai a Zamfara. Ni na fara yi, daga bisani sauran Gwamnoni suka biyo baya.

“Hakan ta faru ne saboda na fahimci harkar tsaro yadda ya kamata,” in ji shi.