Musa Rabiu Kwankwaso, wani ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙalubalanci binciken da wasu hukumomin yaƙi da rashawa uku suke gudanarwa a kansa kan zargi ɗaya kuma a lokaci guda.
Kwankwaso wanda yake tare da tawagar lauyoyinsa ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya amsa gayyatar da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) a ranar Alhamis.
A bayan nan dai ana ta cece-kuce kan wata kwangila wadda ta shafi kai wa ƙananan hukumomin Jihar Kano 44 magunguna.
Cece-kucen na zuwa ne bayan ɓullar wani bidiyo da mai barkwanci nan a dandalan sada zumunta, Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fitar, inda yake zargin Gwamnatin Kano da bai wa wani kamfani na Novomed kwangilar siyan magunguna.
A bidiyon, Dan Bello ya yi zargin gwamnatin Kano da bai wa ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso kwangilar siyan magungunan inda ya ce a duk wata kowace ƙaramar hukuma ta Kano na bayar da naira miliyan tara ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.
Fitar bidiyon ke da wuya, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya ce ba shi da masaniya kan lamarin, ya bayar da umarni ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kan ta gudanar da bincike nan take sannan ta gabatar da rahoto game da hakan domin ɗaukar mataki.
Cikin wata wasiƙa da wani jami’i, CSP Salisu Saleh ya fitar a madadin Shugaban Hukumar PCACC , Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya ce hukumar ta soma bincike inda kawo yanzu an gano naira miliyan 160 daga cikin naira miliyan 440 da ake nema kan kwangilar da ba ta da asali a hukumance.
A jawabinsa, Barista Okechukwu Nwaeze da ke zaman lauyan Musa Garba Kwankwaso, ya ce “hukumomi uku na bincikar mutum ɗaya kan laifi ɗaya kuma a lokaci ɗaya. Ba na tunanin Kundin Tsarin Mulki ya halasta hakan.
“Sau nawa ke nan za mu kare kanmu, sai mun yi hakan sau uku. Saboda haka ana iya wayar gari a samu wani shi ma ya ce yana gayyatarmu.
“Mun fi so kotu ta bayar da sammaci ko ta sanar da matakin da ta ɗauka.
“A halin yanzu muna ci gaba da nazari kan lamarin da duk wani da ya danganci hakan, amma ba zai yiwu a ce hukumomin suna bincike kan laifi guda ɗaya ba.
“Saboda haka za mu ƙalubalanci hakan a kotu.”
Tun bayan soma wannan taƙaddamar ce hukumar ta PCACC ta shiga bincike tare da titsiye wasu jami’an gwamnati ciki har da Babban Sakatare a Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautun Kano, Mohammed Kabawa da Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Kano, Abdullahi Bashir.
Aminiya ta ruwaito cewa an titsiye jami’an gwamnatin ne a ranar Talata da kuma Laraba.