Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce za a yiwa ‘yan sandan da aka kashe a rikicin zanga-zangar #EndSARS karin girma.
Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar wa jami’an ‘yan sanda a lokacin da yake kewayen duba barnar da rikicin yayi a jihar Edo ranar Laraba.
- An kone ofishin ‘yan sanda 5 a Oyo – Kwamishina
- #EndSARS: An kone ofishin ‘yan sanda 2 da na AIT a Edo
A cewar babban Sufetan, za a yi wa kowanne dan sandan da ya rasa ransa a rikicin karin girma zuwa mukamin dake gaba da nasa lokacin da ya rasa ransa.
Yayin rangadin dai Mohammed ya sami rakiyar mataimakin gwamnan jihar Edo, Mista Philip Shu’aibu, tare da wasu manyan jami’an ‘yan sandan jihar.
Ya kuma yi alkawarin cewa rundunar za ta tallafawa iyalan ‘yan sandan da suka rasa rayukansu.
Zauna-gari-banzan dai da suka fake da zanga-zangar sun kona ofishin ‘yan sanda bakwai da motocinsu da dama a jihar ta Edo.