Gwamantin Tarayya za ta yi feshin magani a makarantunta na hadaka a fadin Najeriya a shirye-shiryenta na bude makarantu.
Ministan muhalli, Mohammed Mahmood Abubakar ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Kaduna, yayin jawabi ga ‘yan jarida kan shirin bude makarantun a ranar 4 ga watan Agusta.
Gwamnati za ta bude makarantun ne domin a ba daliban aji uku na babbar sakandare damar shiryawa kafin rubuta jarrabawar WAEC da za su fara ranar 17 ga watan.
A cewarsa, “Za mu tabbatar an yi cikakken feshi ga makarantu kusan 19,000.
“Za mu fara ne da makarantun hadaka na Gwamnatin Tarayya da zarar an kammala shagulgulan Babbar Sallah a shirye-shiryenmu na sake bude su kafin fara jarrabawar.
“Aikin ya hada da yin feshi a dukkanin azuzuwan da za a yi jarabawar bayan kammala kowace jarrabawa”, inji ministan.
Ya ce ma’aikatarsa za ta yi aikin feshin ne tare da hadin gwiwar takwararta ta ilimi.
Ya kuma kirayi iyaye da su tabbatar ‘ya’yansu suna bin dukkanin matakan kariya daga cutar coronavirus ta hanyar yin amfani da takunkumi yayin jarrabawar.
Ministan ya ce za a tabbatar da yin aiki tare tsakanin hukumomin makarantun da aikin ya shafa da jami’an kula da muhallin da za su yi aikin feshin domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ministan ya kuma ce kiyaye tsaftar hannu da ta iskar shaka, kiyaye cunkoson jama’a da kuma bayar da tazara hadi da yin feshi akai-akai ne kadan daga cikin hanyoyin yaki da cutar yayin da duniya ke laluben mafita daga annobar COVID-19.