Wata kotun soji a Burkina Faso ta yanke wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai-da-rai saboda samunsa da laifin kisan tsohon shugaban juyin juya halin kasar, Thomas Sankara a shekarar 1987.
Mutanen da ke zaune a cikin kotun sun kaure da tafi a yayin da suke sauraron hukuncin da alkalin ya shafe lokaci mai tsawo yana karantawa, lamarin da ke kawo karshen shari’ar da ta janyo cece kuce a kasar tsawon shekaru 34.
Kotun ta kuma yanke wa Hyacinthe Kafando, hafsan sojin da ya jagoranci gungun sojojjin da suka kashe Sankara hukuncin daurin rai-da-rai, tare da Gilbert Diendere, wani kwamandan soji mai ci a lokacin kisan gillar da ya zo daidai da lokacin juyin mulkin da ya dora Campaore bisa karagar mulki.
Campaore, wanda ya yi zaman hijira a kasar Ivory Coast bayan zanga zangar da al’ummar kasar suka gudanar ta kifar da gwamnatinsa a shekarar 2014 da Kafando wanda yake hijira tun a shekarar 2016 ba sa nan aka yi musu hukunci.
Dimbim mutane ne suka yi bibiyar wannan shari’ar da aka shafe watanni 6 ana yi a wannan kasa da ke yankin Sahel, wanda kisan Sankara ya ci gaba da kasancewa wani al’amari mara dadin ji a tarihinta.
Sankara, wanda ya yi riko da akidar Markasanci, kuma yake caccakar kasashen yamma, ya gamu da ajalinsa ne a ranar 15 ga watan Oktoban 1987 yana matsayin kaftin din soji mai shekaru 33 sakamakon harbin sa da aka yi da bindiga.
Yadda aka yanke hukuncin gurfanar da Blaise Compaore
Tun a Afrilun 2021 ne Hukumomin Burkina Faso suka yanke hukuncin gurfanar da Blaise Compaore a gaban kotu saboda zargin da ake masa na kashe wanda ya gada, Thomas Sankara a juyin mulkin da ya masa cikin shekarar 1987.
Lauyan marigayi Sankara Guy Herve Kam da ya sanar da matakin ya ce an shigar da kara a gaban kotun soji da ke Ouagadougou bayan da aka tabbatar da tuhumar a kan Compaore da wasu mutane shekaru 34 bayan kisan gillar.
Kam ya ce ana tuhumar Compaore da wasu mutane 13 da laifin cin amanar kasa wadda ta kaiga kisa da kuma kitsa kisan da kuma boye gawarwaki.
Lauyan ya ce lokaci ya yi na tabbatar da gaskiya, kuma ana iya fara shari’ar wadda yanzu haka ake dakon mai gabatar da kara na soji ya sanya ranar fara ta.
Cikin wadanda ake zargi har da Janar Gilbert Diendere, wani tsohon na hannun daman Compaore kuma tsohon kwamandan dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasa lokacin da aka yi juyin mulkin, wanda yanzu haka ya ke cin sarkar shekaru 20 saboda kitsa juyin mulkin da soji suka yi a shekarar 2015.
Lauyan ya ce daga cikin wadanda ake tuhuma wasu sun riga sun mutu, yayin da lauyan Diendere, Mathieu Some ya ce duk da ya ke ba a sanya ranar fara shai’ar ba, ana iya fara ta a kowanne lokaci.