Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar Kaduna ta sanya ranar 17 ga watan Satumba, 2020 domin gudanar da jarrabawar neman guraben karatu a Makarantar Horar da Kanan Hafsoshin ‘Yan Sanda da ke Wudil, karo na takwas.
Kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
- Za a fara tantance masu neman aiki dan sanda ranar Litinin
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan sanda
A cewarsa, daliban da suka fito daga cibiyar zana jarrabawar ta Kaduna za su zauna jarrabawar ce a Makarantar Horar da Malamai ta Kasa (NTI) da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.
“Rundunar ’Yan Sanda da ke Kaduna na sanar da jama’a cewa jarrabawar shiga Makarantar Manyan Jami’an ‘Yan Sanda da ke Wudil a Jihar Kano karo na takwas za ta gudana a ranar 17 ga watan Satumba.
“Saboda haka muke sanar da dukkannin wadanda suka nemi shiga makarantar da su shirya sosai domin jarrabawar da aka shirya gudanarwa ta na’ura mai kwakwalwa wacce kuma za ta gudana a lokaci daya a duk fadin kasa.
“Kazalika rundunarmu na sanar da masu sha’awar shiga cewa za su iya fitar da katin jarrabawarsu ta hanyar amfani da lambar wayarsu da kuma lambobin RRR da za su saka a wurin fitar da katin”, inji kakakin rundunar.