Babbar Kotu a Kasar Kenya a yau Laraba za ta yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito.
Shari’ar da za ta gudana martani ne kan korafin da wani likita ya gabatar a gaban kotun tun a shekarar 2017.
- An karrama Buhari da lambar yabo mafi daraja ta Nijar
- Yaro mafi kiba a duniya ya rage nauyi da kilo 107
A wancan lokacin, likitan ya bayar da hujjar cewa hukuncin haramta yi wa mata kaciya yana cin karo da dokar da ta bai wa kowane jinsin mutane ’yanci da ganin damar abin da za su yi da jikinsu.
Likitan mai suna Dokta Tatu Kamau, ya riki cewa mata suna da damar zuwa asibiti a yi musu wannan al’ada ba tare da fargabar za a kama su ba.
A shekarar 2011 ne Kasar Kenya ta haramta yi wa mata kaciya inda a yanzu ake fargabar wannan kara na iya janyo koma baya ga yunkurin masu fafutikar wannan al’ada ta ci gaba da kasancewa tarihi.