Wata Kotun Musulunci za ta soma sauraron shaidu dangane da shari’ar da ke gabanta kan zargin wani magidanci da yunƙurin yi wa yarinya ’yar shekara 7 fyaɗe a Zariya da ke Jihar Kaduna.
Kotun da ke zamanta a unguwar Tudun Wada ta Zariya, ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba domin sauraron shaidu game da tuhumar da ake yi wa magidancin mai suna Ibrahim Jibrin mai inkiyar Yellow.
- Ambaliya: Adamawa ta ba da tallafin N50m da jiragen ruwa 6 a Borno
- ’Yan bindiga sun sace mata 4 a asibiti a Katsina
Ana dai zargin cewa mutumin mai shekaru 52 ya yi yunƙurin lallaɓar yarinyar da ke zaman makwabtaka da iyayenta domin biyan buƙatarsa.
Sai dai bayan karanto masa ƙunshin tuhumar, magidancin ya musanta zargin da ake yi masa wanda ya saba da sashe na 116 na kundin dokokin shari’a.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Mustapha Muhammad Abdullahi, ya ba da umurnin tsare wanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali kamar yadda sashe na 116 dokokin Jihar Kaduna ya ba shi dama har zuwa ranar 12 ga watan Satumba.
Tun a zaman kotun na farko ne dai aka ɗage sauraron ƙarar, inda daga bisani kotun ta bayar da belin wanda ake zargin a yayin da take dakon samun shawara daga Ma’aikatar Shari’a kan lamarin.
Ana iya tuna cewa, Cibiyar Kula da Cin Zarafin Mata da Ƙananan Yara, watau Salama center da ke Kofar Gayan ce ta binciki lafiyar yarinyar inda ta tabbatar da cewa akwai alamun an yi yunƙurin yin lalata da ita.
A halin yanzu ana ci gaba da kula da lafiyar yarinyar domin kare ta daga kamuwa da wata cuta.