✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a shirya wa dillalan babura taron bita a Jihar Bauchi

Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa na Jihar Bauchi (bIO) Injiniya Muhammed Binni Abdulkadir ya bayyana cewa hukumarsa za ta fara shirya taron bita…

Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa na Jihar Bauchi (bIO) Injiniya Muhammed Binni Abdulkadir ya bayyana cewa hukumarsa za ta fara shirya taron bita ga dillalan da ke sayar tsoffin babura a jihar domin nuna musu illolin da ke tattare da sayen babur din sata a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro a kasar nan.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa ranar Litinin da ta gabata. Ya ce daga yanzu hukumar za ta ci gaba da tsananta bincike a kan manyan hanyoyin jihar domin gano mutanen da suke hawa motoci ba  tare da lamba ba, ko masu amfani da babur ba tare da sun yi rijista da hukumar tara kudaden shiga na gwamnatin jihar ba.
Daga nan ya ce  zai ci gaba da shiga kafafen watsa labarai domin wayar da  al’umma game da yadda za a rika mutunta dokokin hanya a jihar.
“Muna ba da shawara ga dillalan da ke sana’ar sayar da tsoffin babura a jihar da su sani cewa akwai hatsari  mutum ya sayi babur din da babu rijista sannan kuma za mu ci gaba da kama masu karya dokokin hanya,”inji shi.