✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a sayar da kulob din FC Giwa

Alamu sun nuna shirye-shirye sun yi nisa wajen sayar da kulob din FC Giwa da ke Jos.Wani rahoto ya ce tuni kulob din Adamawa United…

Alamu sun nuna shirye-shirye sun yi nisa wajen sayar da kulob din FC Giwa da ke Jos.
Wani rahoto ya ce tuni kulob din Adamawa United da na Kwara United suka fara nuna sha’awar mallakar kulob din. Rahoton ya ce duk da rashin kudin da ya addabi kulob din, shugaban kulob din Chris Giwa ya yi kokari wajen daukar dawainiyarsa ba tare da harkoki sun tsaya cik a kulob din ba.
Kafar watsa labaran wasanni ta Africanfootball.com ta ce kulob din Adamawa United da na Kwara United suka nuna sha’awar saye kulob din don su maye gurbinsa a gasar rukunin firimiya ta Najeriya.
An nuna Chris Giwa ya sanya kulob din a kasuwa ne a tsakanin Naira miliyan 150 zuwa Naira miliyan 300 wato (Dala miliyan daya da rabi).
Rahoton ya ce Chris Giwa ya gaji da daukar dawainiyar kulob din ne bayan ya narka makudan kudi amma kulob din ya kasa samun gurbi a gasar Zakarun Kulob-Kulob na Afirka (Champions League) ko a gasar cin Kofin kalubale na Afirka (Confederations Cup).
Kulob din Adamawa United dai ya kasa hayewa gasar rukunin firimiya ta Najeriya ne a karshen kakar wasa ta bana bayan Filato United ta yi masa kancal a wasan karshe na gasar rukunin ’yan dagaji (Amateur).
Kulob din FC Giwa ya gama a matsayi na biyar ne a gasar firimiya ta Najeriya a kakar wasan da ta wuce.