Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewar akwai yiwuwar samun mummunar ambaliyar ruwa a jihohin Kebbi da Borno da Sakkwato a ’yan kwanaki masu zuwa.
Hukumar ta ci binciken kwararrun masu bincikenta kan yanayin kasa suka gudanar ya nuna cewa jihohin Bayelsa da Delta ma na cikin babbar barazanar ambaliyar.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9, ya jikkata 13 a Bauchi
- Motar bas makare da ’yan sanda ta fada kogi a indiya
Shugaban hukumar na kasa, Farfesa Mansur Matazu, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata yayin wani jawabi ga manema labarai.
Ambaliyar dai yanzu haka tana can tana barna a jihohin Jigawa da Sakkwato sakamakon karuwar ruwan sama, inda daruruwan gidaje da gonaki suka salwanta.
NiMet dai ta ce akwai yiwuwar ci gaba da samun ambaliyar, bisa alkaluman da sakamakon binciken nasu ya nuna.
Ya ce, “Wuraren da suka fi fuskantar barazanar su ne tsakiyar jihar Borno da Arewacin jihohin Sakkwato da Kebbi, ciki har da wani bangare na Kaduna da ma wani sashe Bayelsa da Delta.”
A cewar Shugaban na NiMet, za a sami matsakaiciyar ambaliyar a wasu bangarorin jihohin Kebbi da Zamfara da Neja da Yammacin Kaduna.
Sauran wuraren sune wasu bangarorin jihar Filato da Nasarawa da Taraba da Kudancin Borno da Yobe.
Farfesa Matazu ya kuma ce za a sami ’yar karamar ambaliya a sauran sassan Najeriya.