✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a sake yi wa Abba Kyari gwajin Coronavirus a Legas

A ranar Lahadi ne shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya tafi jihar Legas don sake yi masa gwajin cutar Coronavirus. A wata…

A ranar Lahadi ne shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya tafi jihar Legas don sake yi masa gwajin cutar Coronavirus.

A wata sanarwa da Abba Kyari ya fitar na cewa, “Na tafi Legas ne saboda shawarar likita don karin gwajin da aka yi mani, daga nan sai na dauki wasu matakan gaba, ina cikin koshin lafiya, a makon jiya an gwada ni amma sakamakon ya nuna ina dauke da cutar Coronavirus, wanda ta zama annoba ga duk duniya. Duk na bi umarnin hukumomin da gwamnati don haka na killace kaina.”

Ina son in tabbatar maku cewa, ina daukar duk wasu matakan kare kaina don kaucewa yin barazana ga lafiyar al’umma, mai dauke da wannan cutar yana rayuwa cikin matsi kamar yadda wasu gwajin ke nuna sun kamu da cutar, ban taba yin matsanaicin zazzabi ko kuma wasu alamomin masu dauke da Coronavirus ba, ina ci gaba da aikina daga gida, sannan ina fatan zan koma bakin aikina kamar yadda na saba nan bada dadewa ba.

Abba Kyari, ya ce yana da matasa da kwararru da masana masu kishin kasa wadanda aikin da suke yi ya wuce adadin yadda aka tsare masu suyi na kwanaki bakwai. Za mu ci gaba yi wa Shugaban Najeriya aiki tare da ‘yan Najeriya.

A cikin sanarwar Shugaban ma’akatan fadar shugaban Najeriya, ya ce “Ina yin amfani da wannan damar don gode wa kwararrun jami’an kiwon lafiya na kasar nan, masu kaunar mu abokanan arziki da wasu baki ta yadda suke turo sakonnin jajantawa da fatan alheri.