Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin kashe Naira miliyan 495 wajen sayowa da sanya na’urorin daukar hoton kwakwaf na jikin fasinjoji da kayayyakinsu a tashoshin jirgin kasa da ke jihohin Kano da Kaduna da kuma Abuja.
Minista a Ma’aikatar Sufuri, Ademola Adegoroye ya ce Majalisar Zartarwa ta Kasa ta ba da izinin fitar da kudin domin sayo na’urorin tsaron ne da nufin tabbatar da aminci ga matafiya duba da yanayin tsaro da ake fama da shi a yankin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun sace 20 a Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabon Tsarin CBN Zai Raba Mutane Da Ayyukansu
Ya bayyana cewa hakan na da matukar muhimmanci wajen kare rayuka da kuma ingantawa da saukaka yanayin binciken tsaro a tashoshin jirgin kasan.
Ya ce na’urorin sun hada da wadanda fasinjoji za su bi ta ciki a ga hoton kwakwaf na abin da suke dauke da shi a jikinsu da kuma wadanda za su dauki hoton kwakwaf na jakunkuna da sauran kayan matafiya, sai kuma wadanda jami’un tsaro za su rike a hannu domin caje matafiya.
“Za a yi hakan ne domin hana yiwuwar wani ya shiga jirgin kasan ya yin barna ga matafiya,” in ji ministan.
Idan za a iya tunawa, bayan harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna a 2022 aka kashe fasinjoji 10 aka sace wasu 60, tsohon Ministan Sufuri, Rimi Amaechi, ya alakanta matsalar da rashin cikakken tanadin tsaro ga jirgin kasan.
Ya bayyana cewa a baya ya gabatar wa Gwamnatin Tarayya da bukatar hakan, amma aka yi watsi da ita saboda tsadar kayayyakin tsaron da ya bukaci a samar.