An kafa dokar yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Jihar Neja.
Majalisar Dokokin Jihar Neja ce ta kafa dokar, a wani yunkuri na kawo karshen matsalar ayyukan ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane, da ta yi wa jihar katutu.
Dokar ta wajabta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da hada baki ko taimaka wa masu garkuwa da mutane ko ’yan bindiga da bayanai a fadin jihar.
Majalisar ta amince da dokar ce a zamanta na ranar Talata inda ta yi gyaran fuska ga dokar hukunta masu garkuwa da mutane da barayin shanu ta 2021.
Jihar Neja na daga cikin jihohin da a baya-bayan nan suka fi fama da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane.
A halin yanzu, hukumomin Jihar sun shafe kusan wata guda ana kokarin kubutar da dalibai masu tarin yawa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina.
A baya ’yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai da malamai sama da 40 a Makarantar Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara, kafin daga baya su sako su.
A lokuta daban-daban kuma, ’yan bindiga sun sha satar mutane masu yawa a lokaci guda a sassan Jihar.
A kwanakin baya, an kawo rahoton yadda wasu al’ummomi a wasu kauyukan jihar ke biyan kudade ga ’yan bindiga domin kar su kai musu hari.