An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin nan da ya kashe yarinya ’yar kasa da shekara uku.
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ce ta yanke hukuncin a kan Usman Shehu Bashir bayan ta same shi da laifin yin kisa ta hanyar yi wa yarinyar mai suna Fatima fyade.
A farkon watan jiya ne dai kotun ta dage yanke hukuncin bayan ta bayyana matsayinta game da tuhumar da ake yi wa matashin.
- An dage yanke hukunci kan wanda ya yi wa ’yar shekara 2 fyade
- Amarya ta kashe Angonta don ta zaci fyade zai mata
Da yake bayyana hukuncin, Mai Shari’a Kabir Dabo ya ce dukkan bayanai da hujjojin da ake nema a kan an aikata laifin sun tabbata ta hanyar bayanai da kuma rubutun da ya yi da kansa wanda kotu ta gamsu da su.
Haka nan kuma kotun ta ce hukuncin zai zamo darasi ga masu tunanin aikata irin wannan mummunan laifi na cin zarafin yara kanana nan gaba.
Shari’ar, wadda aka fara ranar 23 ga watan Maris na 2015 ta kawo karshe ne ranar Laraba 3 ga watan Yunin 2020.
Lauyar gwamnatin jihar Kaduna Jummai Dan Azimi ta bayyana gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, mahaifin Fatima, Malam Zakari Ya’u Dahiru ya bayyana hukuncin a matsayin adalci.
Wanda aka yanke wa hukuncin na da damar daukaka kara daga nan har wata uku masu zuwa.