✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za A Rataye Shi Kan Kashe Makwabcinsa Saboda Babur

Babbar kotu da ke Jihar Ekiti ta yanke wa wani mutum mai suna Isma'ila Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe wani saboda babur.

Wata babbar kotu da ke zama a garin Ado Ekiti a Jihar Ekiti ta yanke wa wani mutum mai suna Isma’ila Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe wani mutum mai suna Kareem Abdu, saboda babur.

A ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2018 Isma’ila Ojo ya fara gurfana a gaban kotun, inda alkalin ya tuhume shi da aikata kisa, daga bisani kuma kotun ta same shi da laifin.

Alkalin kotun, Jastis Olusegun Ogunyemi ya bayyana cewa duba da nauyin lafin da kuma hujjojin da aka gabatar, ya gano cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin kisan ta hanyar makure wuyan wanda  ya kashe.

Ya ce, “Wanda ake tuhuma ya aikata laifin, don haka an yake masa hukuncin kisa ta hanyar rataye shi har sai ya mutu.”

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Tunde Arowosola, ya shaida wa kotun cewa wata Agnes Adu ta zo ofishinsu da korafin cewa wani Ismaila Ojo ne ya kashe mijinta a Odo-Uro kan takaddamar mallakar wani babur.

Arowosola ya ce matar ta yi zargin cewa wanda ake ƙara (Ojo) ya shake mamacin.

Har ila yau, dan sanda, Sufeto Lasisi Bashiru, wanda ya shaida wa kotun, ya ce, “Wanda ake tuhumar ya amsa cewa a ranar 13 ga watan Mayun 2018, a lokacin da yake wanka, sai Adu (marigayi) ya zo xaukar babur wanda ya yi amfani da shi kafin ya shiga  wanka ya kuma ajje shi  a kofar gidansa.

“Wanda ake tuhumar ya ce bayan ya gama wanka ya je gidan Adu ya same shi yana barci, duk da haka, wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa bai yi niyyar kashe shi  ba, saboda su biyun sun yi fada ne kawai, kuma babu daya daga cikinsu da ya dauki makami ko ya yi amfani da wani makami ko wani abu makamancin hakan.