✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ragargaje babura 250 da aka kwace a Legas

Gwamnatin Jihar Legas ta ce ta kammala shiri tsaf domin ragargaje babura 250 da ta kwace daga hannun masu karya dokokin hanya a Jihar. Daraktan…

Gwamnatin Jihar Legas ta ce ta kammala shiri tsaf domin ragargaje babura 250 da ta kwace daga hannun masu karya dokokin hanya a Jihar.

Daraktan yada labaran Hukumar Kula da Dokokin Muhalli da sauran laifuka na Jihar, Mista Gbadeyan Abdulraheem ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya raba wa manema labarai ranar Talata.

Ya ce, “Mun kamo mutane da dama, ciki har da na zamani masu tsada, da kuma masu kai wa mutane sakon da suka dauki fasinja duk da akwatin sanya kaya da ke bayan babur din, ko suka cire shi suka dora fasinjan.

“Sai dai wasu daga cikin baburan da muka kama ba su san an kwace musu ba, domin wadanda suka hawo da zarar sun yi arba da jami’anmu gudu suke su bar shi a gurin.

“Sakamakon haka yanzu akwai Babura 250 a hannunmu da za mu nuke su a karshen mako a garin Alausa,” inji shi.

A karshe kakakin ya ja kunnen mamallaka baburan kai kayan da su gargadi mahayasu kan daukar fasinjoji, da kuma bin ka’idojin tuki, domin gudun fadawa hannun hukuma.