Tsohon Antoni-Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, M.A. Lawan, ya bayyana cewa har yanzu Aminu Ado Bayero ne, halastaccen Sarkin Kano, duk da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da aka yanke kan rikicin masarautun jihar.
A wata sanarwa da ya fitar, Lawan ya ce akwai kuskuren fahimtar hukuncin daga ɓangaren Gwamnatin Jihar Kano.
- Gwamnatin Kano ta fara shirin yaƙi da matsalar shara
- Boko Haram sun kashe manoma 40, wasu sun ɓace a Borno
Ya bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta rushe hukuncin da Babbar Kotun Kano, ta yanke na tsige Aminu Ado Bayero daga sarauta.
Ya ƙara da cewa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar ya shafi abubuwa biyu ne kawai.
Na farko, kotun ta rushe hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan ikon sauraron ƙarar, sannan ta rushe hukuncin Babbar Kotun Jihar Kano.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci kan rikicin masarautar jihar.
Bayan hukuncin tsagin gwamnatin jihar, na murna kan ganin cewar hukuncin ya shafe su.
A gefe guda kuma tsagin Aminu Ado Bayero, sun tafi kotun ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.