✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana mika Daliban Afaka ga iyayensu

Daliban da aka kubutar sun isa harabar Kwalejin tare da rakiyar jami'an tsaro.

Saura kiris a hannanta dalibai 27 na Kwalejin Gandun Dajin Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna da aka kubutar daga ’yan bindga ga iyayensu.

A halin yanzu daliban su 27 sun isa harabar makarantar, tare da rakiyar ayarin motocin jami’an tsaro, gabanin a mika su ga iyayen nasu.

Tun gabanin isowar daliban da aka sako makarantar, iyayensu suka taru suna wake-wake da raye-rayen nuna farin cikinsu.

’Yan bindiga sun sako dalibai 27 da suka rage a hannunsu ne a ranar Laraba, bayan shehin malami, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo sun sa baki.

Tattaunawa da ’yan bindigar ta kai sai da aka shigo da wasu da suke jin kunya kafin su sako daliban da suka sace a kwalejin, bayan kwana 57 a hannunsu.