✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako ɗalibin Makarantar Sojin Ruwa da aka sace

An yi aikin haɗin gwiwa tsakanin sojojin ruwa da jami’an Amotekun wajen ceto ɗalibin da mahaifinsa.

Ɗalibin nan mai suna Jethro Onose na makarantar sakandaren sojojin ruwa da ke Imeri a Ƙaramar Hukumar Ose ta Jihar Ondo, ya shaƙi iskar ’yanci bayan makonni biyu a hannun masu garkuwa da mutane.

Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da ɗalibin tare da mahaifinsa, Maliki Onose, yayin da zai mayar da shi makaranta bayan hutun makonni uku.

An yi garkuwa da mutanen biyu ne a tsakanin garuruwan da ke kan iyaka da Ondo da Edo.

Adetunji Adeleye, kwamandan hukumar tsaro wanda aka fi sani da Amotekun Corps a Jihar Ondo ya tabbatar da ceto ɗalibin da mahaifinsa a safiyar Laraba.

Adeleye ya ce, aikin ceto da aka yi tsakanin sojojin ruwa da na Amotekun ne ya sa aka samu nasarar kuɓutar da mahaifin da ɗansa.

“Mun yi aikin haɗin gwiwa tare da sojojin ruwa wajen tattara bayanan sirri.

“Uban da ɗansa yanzu haka sun kuɓuta kuma suna cikin ƙoshin lafiya,” kamar yadda ya shaida wa Aminiya.

Shugaban Ƙungiyar Iyayen Yara (PTA) Damilola Ogunrotimi, na makarantar sakandaren sojojin ruwa, shi ma ya tabbatar da sakin ɗalibin da mahaifinsa.