Fasinjoji 16 da ke cikin wata motar bas ƙirar Toyota Hummer sun ƙone ƙurmus sakamakon haɗarin da ya rutsa da su a kan titin Enugu/Opi/Nsukka da ke yankin Ekwegbe a Ƙaramar Hukumar Igbo-Etiti ta Jihar Enugu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne bayan da motar ta kama da wuta sakamakon afka wa wata katanga da ta yi a kan hanyar.
- Muhammadu Issoufu Ne Ya Kitsa Juyin Mulkin Babana —’Yar Bazoum
- Uba Da Ɗa Sun Hallaka Matar Aure A Edo
Kakakin ‘yan sandan ya ce motar wadda ta ɗauko kayan lambu da sauran kayan abinci haɗarin ya rutsa da ita ne da misalin ƙarfe 5:20 na yammacin ranar Talata.
Ya ce, fasinjojin da suka mutu a haɗarin sun haɗa da maza 14 da mata biyu.
Ya bayyana cewa direban motar wanda ya ɗauko fasinjoji 18 ya ba da shaidar cewa yana tsakar tsala gudu ne sai ya rasa yadda zai yi da motar, lamarin da ya sa afka shingen Jami’ar Maduka da ke kan titin.
Ya ce, “abin takaici ne yadda motar ta kama da wuta kuma ta ƙone matafiyan ƙurmus ta yadda ba a iya gane su.
“A haka muka tattara fasinjojin muka miƙa su asibiti inda a nan aka tabbatar da mutuwarsu.
“Duk da haka, mun ceto wasu fasinjoji biyu da ransu kuma aka kai su asibiti don duba lafiyarsu.
“Jami’an ‘yan sanda da sojoji da kuma ’yan kasa nagari sun taimaka wajen ba da agaji ga fasinjoji.
DSP Daniel ya ce bincike na farko ya nuna motar ta nufi hanyar Nsukka daga kan titin Enugu, amma ba a gano ainihin inda ta tashi da kuma inda ta tsaya ba.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Enugu, Kanayo Uzuegbu, ya ziyarci inda haɗarin ya afku tare da jami’an hukumar kiyaye haɗura domin duba halin da ake ciki.
Kwamishinan ya kuma jajanta wa ‘yan uwa da makusanta waɗanda suka rasu.