✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ƙara mafi karancin albashi zuwa N80,000 a Enugu

An yi ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa N80,000 ga ma'aikatan gwamnatin Jihar Enugu.

An yi ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa N80,000 ga ma’aikatan gwamnatin Jihar Enugu.

Gwamna Peter Mbah ne ya sanar da ƙarin bayan karɓar rahoton kwamitin mafi ƙarancin albashi na jihar.

Ya bayyana cewa an yi ƙarin ne bisa la’akari da muhimmin kula da jin dadin ma’aikata a matsayin ginshikin ci-gaban jihar.

Don haka ya neme su da su ƙara hazaƙa a bakin aikinsu domin yaba wannan tagomashi.

Shugaban Ƙungiyar kwadago ta Kasa (NLC) reshen jihar, Kwamred Fabian Nwigbo yaba wa Gwamnan ganin mafi karancin albashin da ya sanya ya zarce na Gwamnatin Tarayya.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON), Sydney Edeh, ya bayyana fatan cewa za a aiwatar da sanon mafi ƙarancin jihar a matakin ƙananan hukumomi.