Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Sakkwato sun kammala shirye-shiryen kwaso ’yan Jihar kimanin 50,000 da suke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar.
Sanata Ibrahim Gobir, dan Majalisar Dattijai mai wakiltar mazabar Sakkwato ta Gabas ne ya sanar da hakan a zantawarsa da maneman labarai a Sakkwato ranar Lahadi.
- An ci tarar bazawara N55,000 saboda zuwa kabarin mijinta da kare
- ’Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a Anambra
Ya ce akasarin mutanen da za a kwaso ’yan asalin Kananan Hukumomin Sabon Birni da Isa ne da ke Jihar.
Ya ce, “Na samu tattaunawa da mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Karkokin Tsaro, inda na shaida masa cewa har yanzu mutanen suna can.
“Na fada masa har yanzu suna Jamhuriyar Nijar kuma suna bukatar a dawo da su gida.”
Sanata Gobir ya ce ya akwai bukatar bunkasa harkar tsaro gabanin dawo da mutanen gida.
“Na je har garin Tudun Sunnah kwanan nan, sai da na zubar da hawaye saboda na ga mutane sama da 50,000, ciki har da mata da kananan yara ’yan asalin Jihar Sakkwato,” inji Sanata Gobir.
Ya ce ’yan gudun hijirar na zaune a garuruwan Tudun Sunnah da Shada Kwari da Dadada, dukkansu a Karamar Hukumar Gidan Runji da ke Jamhuriyar Nijar.
Ya ce ya ba su gudunmawar buhu 150 na shinkafa da gero da dawa domin rage musu radadin halin da suke ciki, musamman a watan azumin Ramadan.
Sai dai ya koka cewa har yanzu ana ci gaba da kashe-kashe da satar mutane a yankin Gabashin Jihar.